Skip to main content

Posts

Showing posts from February, 2021

MAI KALTUNGO ATTENDED THE FUNERAL PRAYER FOR THE ELDER SON OF EMIR OF FIKA AND THE PRINCE OF FIKA EMIRATE

Uban k'asa Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) da tawaga mai karfi daga masarautan Kaltungo wanda suka hada da Dan'Lawan na Kaltungo, Cikasoron Kaltungo, Sarkin Malaman Kaltungo, Sallaman Kaltungo, Sintalin Kaltungo, da Majikiran Kaltungo sun halacci jana'izan marigayi Alh. Adamu Muhammad Abali (Waziri) wanda shi ne babban d'a ga Uban K'asa Sarkin Fika HRH Alh. Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa (Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Yobe). Alokacin da Uban K'asa Mai Kaltungo yake isar da sakon ta'aziyarsa bayan sallan gawan mamacin, Uban K'asa yayiwa kansa ta'aziya akaron farko, yayiwa Uban K'asa Sarkin Fika ta'aziya da kuma al-ummar masarautan Fika. Uban k'asa Mai Kaltungo yayi nuni dacewa babu mutuwan datafi dagawa mutane hankali irin mutuwar matashi, musamman irin wannan matashi dayake da'babba ga Sarki wanda ko ba'a fad'aba al-umma su

WOMEN IN DA'AWAH NATIONAL HEADQUARTERS ABUJA HAS DONATED FOOD ITEMS, SANITARY PACKS, BEDSHEETS AND MANY OTHER ITEMS TO RECENT VICTIMS OF BILLIRI CRISIS

Kungiyar Mata masu wa'azi ta k'asa wanda akafi sani da (Women in Da'awah National Headquarter) sunyabawa Uban k'asa Mai Kaltungo Engr Saleh Muhammad Umar OON (Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) akan kokarin sa na taimakon yan'gudun hijira wadanda rikicin garin Billiri ya ritsa dasu Kuma suke da sansani a masarautan Kaltungo. Bayanin yabawa Uban kasan yazone ta bakin mai jagorantan kungiyar a karamar hukumar Kaltungo Hajiya Fatima Isyaku Awak alokacin dasuke raba kayan tallafi na abinci, kayan sakawa, takalma, sabulai, omo, taliya, da sauran kayan bukatu na mata a garin Kaltungo, Guguba, Awak da Dogonruwa ga sansanin yan'gudun hijiran wanda uwar kungiyar datake da babban ofishin ta a Abuja ta aiko ta hannun shuwagaban niin Jihar Gombe. Shuwagaban nin mata a sansani gudu hudu dasuke cikin masarautan Kaltungo sun karbi kayan tallafin tareda mika godiyan su na musamman ga yan'uwa dasuka taimaka musu, sun mika godiyan

MAI KALTUNGO VISITED REFUGEES OF BILLIRI CRISIS IN DOGONRUWA AND AWAK KALTUNGO CHIEFDOM

Uban k'asa Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) ya ziyarci yan'gudun hijira asafiyar yau a garin Dogonruwa da Awak don ganin halin dasuke ciki tareda jajantawa juna abun dayafaru na rikici da hatsaniya a garin Billiri. Uban k'asa ya jawo hankulan al-umma dasu guji dukkan wani rikici ko hatsaniya, yin rikici baya haifar da wani cigaba ga al-umma. Dukkan abunda zaman lafiya bai haifar ba rashin sa bazai haifar ba. Uban k'asa yayi addu'an Allah yakawo karshen wannan rikici, Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya, wadanda sukayi hasaran dukiyoyin su Allah ya mayar musu da mafi alheri.

MAI KALTUNGO YA YABAWA GOMNATIN JIHAR GOMBE NA KAWO TALLAFI GA YAN'GUDUN HIJIRA CIKIN GAGGAWA

Uban k'asa Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) ya sheda rabawa yan'gudun hijira daga garin Billiri zuwa cikin garin Kaltungo kayan tallafi da gomnan Jihar Gombe Alh. Muhammadu Inuwa Yahaya ya aiko ta hannun shugaban karamar hukumar Kaltungo Alh. Faruq Aliyu Kabo. Za'a raba kayan ne ga yan'gudun hijira na rikicin daya barke a garin Billiri, dayawa daga cikin yan'gudun hijiran sunyi sannani ne acikin garin Kaltungo, Kamo da Dogonruwa. Shugaban karamar hukumar Kaltungo zai jagoranci raba kayan tallafin ga wadannan sannanoni uku dukkan su acikin masarautan Kaltungo. Uban k'asa ya yabawa gomnatin Jihar ta Gombe na kawo wannan tallafi cikin gaggawa. Mai Kaltungo yayi nuni dacewa lallai wannan shi ne abunda ake bukata ga shugaba. Uban k'asa yabshawarci wadanda alhakin raba kayayyakin tallafin ya doru akansu dasuyi adalci wajen rabon kayan.

MAI KALTUNGO YA ZIYARCI SANSANIN YAN'GUDUN HIJIRA DAGA BILLIRI

Uban k'asa Mai Kaltungo dottijon arziki mai tausayin talakawa ya ziyarci yan'gudun hijira daga garin Billiri zuwa masarautan Kaltungo asafiyar yau. Bayan karban yan'gudun hijiran da ciyaman na karamar hukumar Kaltungo Alh. Faruq Aliyu Kabo yayi a jiya Uban k'asa ya ziyarci yan'gudun hijiran don taimaka musu da basu kalamai na rarrashi. Uban k'asa ya bayyana rashin jin dadinsa a faruwan wannan abu dakuma halin da al-umma suka jefa kansu. Uban k'asa yayi nuni kan muhimmacin zaman lafiya, wanda yake cewa idan babu zaman lafiya babu wani abu na cigaba dazai iso al-umma. Uban k'asa yayi fata da addu'an Allah yakawo karshen wannan iftila'i, sannan kuma ya jawo hankulan al-umma dasu kara kai zuciya nesa, kowa ya zauna da dan'uwansa lafiya.

MAI KALTUNGO ATTENDED THE 2021ANNUAL CONFERENCE OF THE UNITED METHODIST CHURCH IN NIG. NORTHERN NIG. WOMEN DIVISION

Uban k'asa Mai Kaltungo ya halacci taron matan hadaddiyar ekilisiya Mai tsari a Najeriya, Majalisan arewa na shekara shekara a kauyen Jauro Sajo cikin garin Filiya karamar hukumar Shongom ta masarautan Kaltungo. Alokacin dayake jawabin sa amatsayin sa n'a Uban k'asa, Mai Kaltungo ya yabawa kokari/ayyukan da ekilisiyan suke gudanarwa wanda yazo daidai da ire iren ayyukan da masarautan Kaltungo tamaida hankali wajen yi na wazar da sakon zaman lafiya tsakanin al-umma da fadawa al-umma gaskiya komai dacinta. Uban k'asa yakarawa shuwagabanni da membobin ekilisiyan karfin guiwa na cigaba da aikata ayyukan alheri dasuke gudanarwa. Daga karshen Uban k'asa yayiwa ekilisiyan fatan alheri da sanya musu albarka na iyayen k'asa.

MAI KALTUNGO CONDOLÉD THE EMIR OF HADEJIA OVER MOTHER DEATH

Uban K'asa Mai Kaltungo Engr. Daleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) ya ziyarci fadar k'asar Hadejia don ta'aziya na rasuwan Hajiya Khadija Abdulkadir (Mai Babban Daki) mahaifiya ga HRH Alh. (Dr.) Adamu Abubakar Maje Haruna Sarkin Hadejia kuma Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Jigawa. Alokacin dayake isar da sakon ta'aziyarsa ga Sarkin Hadejia da al-ummar masarautan Hadejia, Uban k'asa Mai Kaltungo ya nuna alheninsa na wannan rashi, Uban k'asa yayi nuni dacewa mutuwar mahaifiya babban rashine amma al-amari na ubangijine wanda dukkan mu lokaci muke jira Dayake maida jawabin godiya amadadin shikansa da masarautan Hadejia Sarkin na Hadejia ya nuna godiya, jindadi dakuma farin ciki bisaga ziyaran da kuma ta'aziya da Uban k'asa ya kawo musu. Uban k'asa ya bukaci Mai Kaltungo ya ziyarci fadar ya Hadejia awani lokaci bawai sai irin wannan abu ya faruba. Sarkin na Hadejia yayiwa

AL-SHEIK HAMDI MUHAMMAD OF QATAR CHARITY FOUNDATION PAY HOMAGE TO MAI KALTUNGO

Wakilin kungiyar taimako na k'asar Qatar Al-sheik Hamdi Muhammad ya ziyarci fadar Uban k'asa Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe). Kungiyar ta k'asar Qatar sun shaharane wajen kokarin gina masallatai, bohula, makarantu da sauransu. Ziyaran na Al-sheik Hamdi Muhammad yanada alakane da ginin masallacin fadar Uban k'asa Mai Kaltungo. Babban abunda yabawa Al-sheik Hamdi sha'awa kuma ya burgeshi bayan kammada zagaya masallacin tareda rakiyan Uban k'asa, Madakin Kaltungo da Injiniya Mai kulada ginin masallacin wato Wamban Kaltungo wanda sanadiyar hakan yayiwa Uban k'asa da al-ummar k'asar Kaltungo alkawarin isar da koken masallacin ga shugaban su kuma zaiyi iyakacin kokarinsa wajen bibiya harsai ankammala ginin masallacin shi ne ganin yadda masarautan Kaltungo da al-ummar k'asar Kaltungo sukayi kokari har ginin masallacin yakai ga inda yake. Uban k'asa yay

MAI KALTUNGO PAY A ROYALTY VISIT TO EMIR OF BAUCHI

Uban k'asa Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) ya ziyarci fadar Uban k'asa Sarkin Bauchi HRH Alh. Rilwanu Suleimanu Adamu CFR (Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Bauchi) don sada zumumci da caffan bargirma tareda godiya na mutumta Jihar Gombe akowani lokaci .Mai Kaltungo ya yabawa Sarkin na Bauchi kan kokarin sa na amsa gayyatan Jihar Gombe akowani lokaci musamman akan abubuwan dasuka shafi masarautu a Jihar Gombe da kewayenta. Uban k'asa Sarkin Bauchi ya yabawa Mai Kaltungo akan halayensa na ziyarce ziyarce ciki da wajen Najeriya don inganta zumumci tsakanin Sarakuna, Sarkin na Bauchi yakara da yabawa Mai Kaltungo akan kokarin sa na kula da al-adu da hada kan al-umma don wanzar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin  k'asa dama fadin Najeriya. Sarkin Bauchi yayiwa Mai Kaltungo fatan alheri da addu'an Allah yakarawa sarki lafiya da nisan kwana.