WOMEN IN DA'AWAH NATIONAL HEADQUARTERS ABUJA HAS DONATED FOOD ITEMS, SANITARY PACKS, BEDSHEETS AND MANY OTHER ITEMS TO RECENT VICTIMS OF BILLIRI CRISIS
Kungiyar Mata masu wa'azi ta k'asa wanda akafi sani da (Women in Da'awah National Headquarter) sunyabawa Uban k'asa Mai Kaltungo Engr Saleh Muhammad Umar OON (Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) akan kokarin sa na taimakon yan'gudun hijira wadanda rikicin garin Billiri ya ritsa dasu Kuma suke da sansani a masarautan Kaltungo.
Bayanin yabawa Uban kasan yazone ta bakin mai jagorantan kungiyar a karamar hukumar Kaltungo Hajiya Fatima Isyaku Awak alokacin dasuke raba kayan tallafi na abinci, kayan sakawa, takalma, sabulai, omo, taliya, da sauran kayan bukatu na mata a garin Kaltungo, Guguba, Awak da Dogonruwa ga sansanin yan'gudun hijiran wanda uwar kungiyar datake da babban ofishin ta a Abuja ta aiko ta hannun shuwagaban niin Jihar Gombe.
Shuwagaban nin mata a sansani gudu hudu dasuke cikin masarautan Kaltungo sun karbi kayan tallafin tareda mika godiyan su na musamman ga yan'uwa dasuka taimaka musu, sun mika godiyan su ga uwar kungiyar ta mata masu gudanar da wa'azi. Sun karkare godiyan nasu ne ga Uban K'asa Mai Kaltungo na kokarin dayayi musu tundaga faruwan wannan rikici dakuma ire iren tallafi da gomnatin Jihar Gombe takawo musu, sun karkare godiyan nasu ga hakimai wadanda suka basu masaukai, .
Comments
Post a Comment