GOMBE STATE TASK FORCE ON COVID-19; THE SUB-COMMITEE ON ADVOCACY AND SENSITIZATION CHAIRED BY MAI KALTUNGO ON AN ADVOCACY TOUR TO RELIGIOU LEADERS, AND WOMEN GROUPS OF KALTUNGO/SHONGOM, BILLIRI AND AKKO L.G.A
Mataimakin Shugaban Kwamitin aiki da cikawa akan cutar Korona Bairos a jihar Gombe, kuma Shugaban Kwamitin Fad'akarwa da Wayar da kan al-umma akan cutar Korona Bairos, Mai Kaltungo, Engr. Saleh Muhammad Umar OON da membobin kwamitin nashi da suka had'a da; Hon. Bappah Jurara (Chairman Committee on Health), Hon. Na'omi J.J Awak (Kwamishiniyar ma'aikatan mata, walwala da cigaba), Hon. Madam Briskila Tanko (Malafar Kaltungo), Rev. Samuel Bulus (Deputy CAN Chairman), Alh. Saleh Danburan (Secretary JNI Gombe State), Sallau Muhammad Malami (State Health Educator GSPHCDA) sun zagaya don yawar da kan al-umma akan cutar Korona Bairos.
Kwamitin karkashin jagorancin Mai Kaltungo sun fara ziyaran wayar da kan ne da kuma fad'akarwa daga fadan uban gayyan Mai Kaltungo acikin karamar hukumar Kaltungo/Shongom daganan kwamitin sun dunguma zuwa karamar hukumar Billiri da Akko. Babban manufan kwamitin shi ne wayar da kan al-umma da kuma jaddada musu kancewa lallai akwai cutar Korona Bairos.Kwamitin yayi kokarin ganawa da b'angarorin Limaman addinai (musulmi da kirista), da kuma b'angaren mata (Zumuntan mata da FOMWAN) a kananan hukumomin na Kaltungo/Shongom, Billiri da Akko.
Ganin muhimmancin da wad'annan b'angarori suke dashi wajen tarbiya da kuma wayar da kawunan al-umma musamman mabiya, yasanya kwamitin bada muhimmanci wajen gayyatan b'angagori na addinai. Kusancin da limaman addinai suke dashi da al-umma abune wanda yafi karfin misaltawa.
Dayake jawabin sa shugaban kwamitin Engr. Alh. Saleh Muhammad Umar OON (Mai Kaltungo) yajawo hankulan limaman addinai dasu kasance masu wayar da kan al-umma humimmancin tsaftace muhallinsu, bada tazara yayin mu'amala, sanya sumbatta, kokari wajen wanke hannuwa da sabulu da kuma ruwa mai gudana, sanar da hukumomi cikin gaggawa idan anga wani ko wata da alamomi na cutar Korona Bairos da sauran matakai da masana suke gayanama.
Hon. Bappah Jurara (Shugaban kwamitin Lafiya na majalisan wakilai na jihar Gombe) da Hon. Na'omi J.J Awak dukkan su membobi ne a kwamitin kuma anasu gudumawar sunyi sokaci kan muhimmancin iyalai suyi kokari wajen wayar wa junansu kai, da kuma kare kawuwan mu daga kamuwa daga wannan cuta ta Korona Bairos. Sunyi kira dacewa abune mai kyau ayi himma wajen biyayya akan dokokin da gomnati ta tanadar da kuma masana a b'angaren lafiya don kare kanmu daga kamuwa da wannan cuta.
Comments
Post a Comment