Uban k'asa Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) ya ziyarci fadar Uban k'asa Sarkin Bauchi HRH Alh. Rilwanu Suleimanu Adamu CFR (Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Bauchi) don sada zumumci da caffan bargirma tareda godiya na mutumta Jihar Gombe akowani lokaci.Mai Kaltungo ya yabawa Sarkin na Bauchi kan kokarin sa na amsa gayyatan Jihar Gombe akowani lokaci musamman akan abubuwan dasuka shafi masarautu a Jihar Gombe da kewayenta.
Uban k'asa Sarkin Bauchi ya yabawa Mai Kaltungo akan halayensa na ziyarce ziyarce ciki da wajen Najeriya don inganta zumumci tsakanin Sarakuna, Sarkin na Bauchi yakara da yabawa Mai Kaltungo akan kokarin sa na kula da al-adu da hada kan al-umma don wanzar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin k'asa dama fadin Najeriya.
Comments
Post a Comment