Uban k'asa Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) ya ziyarci yan'gudun hijira asafiyar yau a garin Dogonruwa da Awak don ganin halin dasuke ciki tareda jajantawa juna abun dayafaru na rikici da hatsaniya a garin Billiri.
Uban k'asa ya jawo hankulan al-umma dasu guji dukkan wani rikici ko hatsaniya, yin rikici baya haifar da wani cigaba ga al-umma. Dukkan abunda zaman lafiya bai haifar ba rashin sa bazai haifar ba. Uban k'asa yayi addu'an Allah yakawo karshen wannan rikici, Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya, wadanda sukayi hasaran dukiyoyin su Allah ya mayar musu da mafi alheri.
Comments
Post a Comment