First of it's kind; Lapantun Festival. Akaro na farko a tarihin masarautan Kaltungo, Uban kasa Mai Kaltungo ya gudanar da bikin al-adu a Dutsen Goggo dake garin Ture Lapantun cikin masarautan Kaltungo. Akwai ababen mamaki da dumbin arziki da Allah ya ajiyesu a masarautan Kaltungo wanda Uban kasa Mai Kaltungo yake kokari babu dare babu rana wajen nuna wa al-ummarsa hakan. Kasancewar Allah ya ajiye bawansa a cikin daji ko kauye hakan bawai yana nufin wanda suke zaune cikin birane sun fisu da wani abu bane. Kwanakin baya Uban kasa yayi ziyara zuwa kauyen Lapantun wanda take gundumar Ture cikin masarautan Kaltungo, ayayin ziyaran Uban kasa ya ganewa idon sa irin dumbin ababen sha'awa tareda jawo hakulan masu yawon bude ido da neman ilimi. Dalilin haka, Uban kasa ya shirya don ziyartan wannan kauye akaro na biyu tareda al-umma don kara kulla donkon zumumci, jawo al-umma mazauna kauyuka kusa da masarauta da nuna musu muhimmacin zaman lafiya.
MAI KALTUNGO ATTENDED THE FUNERAL PRAYER FOR THE ELDER SON OF EMIR OF FIKA AND THE PRINCE OF FIKA EMIRATE
Uban k'asa Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) da tawaga mai karfi daga masarautan Kaltungo wanda suka hada da Dan'Lawan na Kaltungo, Cikasoron Kaltungo, Sarkin Malaman Kaltungo, Sallaman Kaltungo, Sintalin Kaltungo, da Majikiran Kaltungo sun halacci jana'izan marigayi Alh. Adamu Muhammad Abali (Waziri) wanda shi ne babban d'a ga Uban K'asa Sarkin Fika HRH Alh. Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa (Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Yobe). Alokacin da Uban K'asa Mai Kaltungo yake isar da sakon ta'aziyarsa bayan sallan gawan mamacin, Uban K'asa yayiwa kansa ta'aziya akaron farko, yayiwa Uban K'asa Sarkin Fika ta'aziya da kuma al-ummar masarautan Fika. Uban k'asa Mai Kaltungo yayi nuni dacewa babu mutuwan datafi dagawa mutane hankali irin mutuwar matashi, musamman irin wannan matashi dayake da'babba ga Sarki wanda ko ba'a fad'aba al-umma su