First of it's kind; Lapantun Festival.
Akaro na farko a tarihin masarautan Kaltungo, Uban kasa Mai Kaltungo ya gudanar da bikin al-adu a Dutsen Goggo dake garin Ture Lapantun cikin masarautan Kaltungo.
Akwai ababen mamaki da dumbin arziki da Allah ya ajiyesu a masarautan Kaltungo wanda Uban kasa Mai Kaltungo yake kokari babu dare babu rana wajen nuna wa al-ummarsa hakan. Kasancewar Allah ya ajiye bawansa a cikin daji ko kauye hakan bawai yana nufin wanda suke zaune cikin birane sun fisu da wani abu bane.
Kwanakin baya Uban kasa yayi ziyara zuwa kauyen Lapantun wanda take gundumar Ture cikin masarautan Kaltungo, ayayin ziyaran Uban kasa ya ganewa idon sa irin dumbin ababen sha'awa tareda jawo hakulan masu yawon bude ido da neman ilimi. Dalilin haka, Uban kasa ya shirya don ziyartan wannan kauye akaro na biyu tareda al-umma don kara kulla donkon zumumci, jawo al-umma mazauna kauyuka kusa da masarauta da nuna musu muhimmacin zaman lafiya.
Uban kasa ya ya jawo hankulan matasa dasu kasance masu bin doka da oda, idan gomnati ta keba wannan daji dolene matasa su kasance masu kiyaye duk dokan da aka sanya don gudu tare da tsira tare. Uban kasa ya hori matasan da cewa sukara rungumar zaman lafiya da sana'oi don kaucewa fadawa hannayen bata gari.
Comments
Post a Comment