Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakunan Jihar Gombe) ya ziyarci fadan Zazzau don yiwa kansa, iyalan marigayi Sarkin Zazzau, al-ummar masarautan Zazzau da gomnatin Jihar Kaduna ta'aziyan rasuwan mahaifi kuma suruki gareshi marigayi HRH Alh. (Dr.) Shehu Idriss (Sarkin Zazzau).
Sadaukin Zazzau shiya jagorancin tawagan Mai Kaltungo zuwa kushewan marigayin don yimasa addu'a ta musamman wanda babban limamin masalllacin fadan Kaltungo ya jagoranta.
Ayayin jawabinsa Mai Kaltungo ya bawa kansa, iyalan marigayin, al-ummar masarautan Zazzau da gomnatin Jihar Kaduna hakurin wannan babban rĂ shi. Mai Kaltungo yayi nuni dacewa mutuwa abune dake kan kowa kuma ba sabon abune atsakanin mu, amma saboda juna akewa jimami dakuma irin rawa da muhimmanci Wanda marigayin yake dashi atsakanin al-umma.
Daga karshen Mai Kaltungo yayi addu'an Allah yajikan marigayin ya kyautata makomansa, yayi addu'an Allah yasanya albarka acikin zuriyarsa daya bari abaya.
Comments
Post a Comment