Mai Kaltungo Engr Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakunan Gargajiya na Jihar Gombe) yayi ziyara tareda manya manyan hakiman sa zuwa masarautan Kano.
Ziyaran yanada alakane da taya sabon Sarkin na Kano Alh Aminu Ado Bayero murnan samun sarautan kasar ta Kano dakuma Kara kulla dankon zumumci tsakanin masarautan Kano da Kaltungo.
Babu shakka ziyaran yabada ma'ana ta inda Mai Martaba Sarkin na Kano Alh Aminu Ado Bayero ya tabbatar da irin alaka da yan'uwan taka dake tsakanin masarautan Kano dana Kaltungo
Sarkin na Kano ya kara tabbatar da cewa ashirye masarautan Kano take don ziyartan kasar Kaltungo dama sauran masarautu don Kara kulla dankon zumumci tsakanin Sarakuna iyayen kasa
Sarkin na Kano ya yabawa Mai Kaltungo akan irin wannan aiki dayakeyi na ziyara. Babu shakka Mai Kaltungo yasanu shedan ziyara tsakanin sarakuna a fadin kasa Nigeria.
Comments
Post a Comment