COVID-19; K'ARAMIN KWAMITIN FAD'AKARWA NA AIKI DA CIKAWA AKAN CUTAR KORONA BAIROS TA KAMMALA ZIYARAN RANGADIN TA DA KANANAN HUKUMOMIN GOMBE DA DUKKU
K'arkashin jagorancin kwamishiniyar ma'aikatan mata, walwala da cigaban matan na jihar Gombe Hon. Na'omi J.J Awak, kwamiti mai membobi bakwai ya kammala rangadin sa na fad'akarwa da wayar da kan al-umma akan cutar COVID-19 ayau da kananan hukumomin Gombe da Dukku.
Tunda farkon fari shugaban wayar da kan al-umma acibiyar lafiya mataki na farko a jihar Gombe Alh. Sallau Malami ya bayyanawa mahalarta taron muhimmancin dasuke dashi acikin al-umma wanda hakan yasanya kwamitin zakulosu don taimakawa gomnati wajen yakar cutar ta Korona Bairos a jihar Gombe.
Dalili daga cikin dalilan dayasanya k'irk'iran wannan kwamitin yanada alaka sa fad'akar/ k'ara wayar da kan shugabannin addinai don suma su fad'akar/wayar da kan mabiyan su daga kowani b'angare.
Malaman addinai daga b'angaren kiristoci da musulmi sun yaba dakuma jinjinawa kwamitin kan samar dasu amatsayin wad'anda sukafi dacewa don ganin kusancinsu da al-umma. Babban tabbacin da zasuyi bawa gomnati shi ne Isar da sakon dakuma cigaba da wayar da kan al-umma akan cutar ta COVID-19.
Shugaban kwamitin Hon. Na'omi J.J Awak a jawabin ta godiya tayiwa shugabannin addinai da suke goya wa gomnati baya adukkanin shirye shiryen ta na cigaba, kare rayuka da lafiyan al-ummar jihar Gombe.
Hon. Na'omi tak'ara da yabawa shugabannin addinai akan namijin kokarin dasukayi wajen fad'akar da mabiyan su muhimmancin biyayya ga dukkan dokan da gomnati takawo matukar bai sab'awa addini ba.
Daga k'arshen Hon. Na'omi tayi fatan alheri da addu'an ganin k'arshen wannan cuta a jihar Gombe, Najeriya da fad'in duniya gaba d'aya.
Comments
Post a Comment