COVID-19, HON. NA'OMI J.J AWAK LEAD THE SUB-COMMITEE ON ADVOCACY AND SENSITIZATION TO A TOUR VISIT TO BALANGA AND Y/DEBA L.G.A
Hon. Na'omi J.J Awak (Kwamishiniyar mata, walwala da cigaban matan jihar Gombe) ta jagoranci kwamitin fad'akarwa da wayar da kan al-umma akan cutar COVID-19 wanda kwamitine mai membobi daya had'a da; Hon. Bappah Jurara (Member and Chairman Committee on Health), Hon. Madam Briskila Tanko (Malafar Kaltungo), Dr. Yusuf Usman (Deputy State Epidemiologist), Rev. Samuel Bulus (Deputy CAN Chairman), Alh. Saleh Danburan (Secretary JNI Gombe State), Sallau Muhammad Malami (State Health Educator GSPHCDA) zuwa rangadi kananan hukumomin Balanga (Talasse) da Y/Deba don fad'akar da shugabannin addinai da k'ungiyoyin mata akan cutar Korona Bairos (COVID-19).
Babban abunda kwamitin ya maida hankali wajen fad'akarwan shi ne yadda shugabannin addinai zasu taka rawa mai muhimmanci wajen wayar da kan mabiya mabanbanta juna muhimmancin kare kawunan su daga kamuwa dakuma yaduwan cutar COVID-19.
Matakan kariya dasuka had'a da sanya takunkumi, bada tazara, wanke hannaye da sabulu wajen ruwa mai gudana, gujewa tarurruka na aure, suna da sauransu, bada himma wajen sanar da hukumomi bullan cutar ko alamomin cutar ga wani ko wata, kai rahoton dawowan wani matafiyi dayadawo kuma akaga alamomin cutar sun bayyana. Wasu daga cikin shugabannin addinai dasuke maida jawabi sun yabawa kwamitin dayin wannan tunani na sanya shugabannin addinai acikin wannan lamari, sun k'ara dacewa a b'angaren shugabannin addinai sunayin iyakan kokarin su wajen fad'akar da al-umma, babban abunda suke fatan samu wajen hukumomi shi ne k'arfafawa.
Comments
Post a Comment