Skip to main content

Posts

Showing posts from September, 2020

Mai Kaltungo ya sheda addu'an Uku na Sarkin Zazzau a fadan kasar Zazzau

Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakunan Jihar Gombe) da tawagarsa sun sheda addu'an uku na marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau HRH Alh (Dr.) Shehu Idriss CFR. Angudanar da addu'oi na musamman na Allah ya jikan Sarki, da addu'an Allah yaraya zuriyan da marigayin ya bari.taron addu'an ya gudana ne a farfajiyan masarautan Zazzau wanda yasamu kulawa da tsaro na musamman. Taron addu'an yasamu halattan manyan baki dasuka hada da; tsohon Shugaban k'asa Chief Olusegum Obasanjo, gomnan jihar Kaduna Mal. Nasir Ahmad El-Rufa'i, gomnan jihar Jigawa, manya sarakuna da yan'siyasa daga ciki da wajen Jihar Kaduna.

MAI KALTUNGO YAYIWA IYALAN MARIGAYI SARKIN ZAZZAU, AL-UMMA, DA GOMNATIN KASAR ZAZZAU TA'AZIYA

Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakunan Jihar Gombe) ya ziyarci fadan Zazzau don yiwa kansa, iyalan marigayi Sarkin Zazzau, al-ummar masarautan Zazzau da gomnatin Jihar Kaduna ta'aziyan rasuwan mahaifi kuma suruki gareshi marigayi HRH Alh. (Dr.) Shehu Idriss (Sarkin Zazzau). Sadaukin Zazzau shiya jagorancin tawagan Mai Kaltungo zuwa kushewan marigayin don yimasa addu'a ta musamman wanda babban limamin masalllacin fadan Kaltungo ya jagoranta. Ayayin jawabinsa Mai Kaltungo ya bawa kansa, iyalan marigayin, al-ummar masarautan Zazzau da gomnatin Jihar Kaduna hakurin wannan babban rĂ shi. Mai Kaltungo yayi nuni dacewa mutuwa abune dake kan kowa kuma ba sabon abune atsakanin mu, amma saboda juna akewa jimami dakuma irin rawa da muhimmanci Wanda marigayin yake dashi atsakanin al-umma. Daga karshen Mai Kaltungo yayi addu'an Allah yajikan marigayin ya kyautata makomansa, yayi addu'an Allah

Rotary International District 9125 Pay Homage to Mai Kaltungo

The Rotary International District 9125 under the leadership of the District Governor Mrs. Jumoke Bamigboye accompanied by  the Former Military administrator Bauchi State Theophilus Bamigboye, pay homage to Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Deputy Chairman Gombe State Council of Emirs and Chiefs). The essence of the homage is to greet, seek for a fatherly blessings from Mai Kaltungo, commission a solar powered borehole in Lapandimtai Community of Kaltungo LGA, by the Nigeria National Polio Plus Commitee, plant tress in UBEC Vocational Training Centre Kaltungo by the club and also to see some areas that may require the club to keep supporting. Mai Kaltungo in his remarks commended the Rotary Club and the kind of support they delivered to complement the government effort. He urged the rotary club to keep doing their good work in the society. The sole aims of rotary club is to Protect Environment, Maternal and child, Basic education and literac

MAI KALTUNGO DA TAWAGARSA SUNYI ZIYARA GARIN BIU DON TA'AZIYA NA RASUWAN SARKIN BIU

Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakunan Jihar Gombe) da tawaga wacce ta hada da; Hakimin Awak, Sa'in Kaltungo, Cikasoron Kaltungo, Maidalan Gombe, Salaman Kaltungo, da Sintalin Kaltungo sunyi ziyaran ta'aziya zuwa fadan k'asar Biu ta jihar Borno na rasuwan HRH Alh. Mai Umar Mustapha Aliyu CON, (Sarkin Biu)., Sarkin na Biu ya kwashe shekaru 31 akan gadon sarautan kasar ta Biu kuma yarasu yana mai shekaru 79 aduniya. HRH Alh Dr. Shehu Hashimi II Ibn Umar El-Kanami (Shehun Damaturu) shiyakasance mai karban gaisuwa amadadin iyalan marigayi. Mai Kaltungo ya bayyana mariyayin amatsayin dottijo kuma abokin shawara da dinke dukkan wata b'arak'a tsakanin Sarakuna, Mai Kaltungo ya ayyana rasuwan Sarkin amatsayin babban rashi ga k'asa gaba daya kuma ya mika ta'aziyan masarautan sa ga iyalan marigayin, masarautan Biu da gomnatin jihar Borno.